Ancelotti zai halarci wasan da Chelsea za ta buga da Arsenal

Carlo Ancelotti
Image caption Carlo Ancelotti

Kocin Chelsea zai halarci wasan da Chelsea za ta buga da Arsenal ranar lahadi a filin Stamford Bridge bayan rasuwar mahaifinsa .

Mahaifinsa Giuseppe ya rasune a daren ranar talata yana shekaru tamanin da bakwai da haihuwa. "Daukacin jama'ar Chelsea na mika ta'aziyarsu ga iyalin kocin kungiyar Carlo, saboda rasuwar mahaifinsa." In ji wata sanarwa da kungiyar ta buga a shafin ta na Intanent.

Mataimakin kocin kungiyar Ray Wilkins ne zai gana da manema labarai kafin wasan a ranar Juma'a.