Et'o ya ce Benitez ya fi Mourinho

Image caption Samuel Eto'o

Dan wasan Inter Milan Samuel Eto'o ya ce sabon kocin kungiyar Rafael Benitez ya fi sanin yada ake tafiyar da 'yan wasan gaba, bisa tsohon kocin kungiyar Jose Mourinho.

Dan wasan ya zura kwallaye uku ne a wasan da kungiyar ta doke Werder Bremen da ci hudu da nema a gasar zakarun Turai da aka buga a daren jiya.

Dan wasan dai ya zura kwallaye 11 a wasanni tara daya buga a kakar wasan bana.

"A lokacin da Mourinho ya ke horon mu muna yawan tsaya bayane domin mu kare gida, sai dai mu rika zaburan neman ci amma Benitez daga farkon wasa zuwa karshen ta yana samu kai hare hare ne babu kaukautawa, wanda kuma yake bamu damar zura kwallaye.