Ban yi ritaya ba-In ji Didier Drogba

Drogba
Image caption Didier Drogba na Ivory Coast

Kaptin din Ivory Coast Didier Drogba ya karyata rahotannin dake cewar ya yi ritaya daga bugawa kasarshi kwallon.

Wasu kafafen yada labarai a Ivory Coast sun bayyana cewar dan kwallon Chelsea ya yi ritaya saboda tunda aka fara wasanni share fage na gasar kasashen Afrika bai buga ba.

Dan shekaru talatin da biyun bai taka leda ba a wasansu da Rwanda sannan kuma bai shiga cikin tawagar 'yan kwallon ashirin da koch Francois Zahoui ya gayyata don karawa da Burundi.

Drogba yace"ina hutawa ne kawai amma idan aka kira ni a wasanni na gaba zan zo"

Drogba ya kasance dan kwallon Ivory Coast da yafi kowanne zira kwallaye a tarihi inda kawo yanzu ya ci kwallaye 45.