CAF :TP Mezembe da Al Ahly sun kama hanyar daga kofi

Caf
Image caption Kofin da kungiyoyin Afrika ke takara akai

Mai rike da kofin gasar zakarun Afrika TP Mazembe ta Kongo na kan hanyarta na kara lashe gasar bayan ta samu galaba akan JS Kabylie ta Algeriya daci uku da daya a bugun farko na zagayen kusada karshe.

Kungiyar Al Ahly ta Masar wacce ta lashe gasar sau shida ta casa Esperance ta Tunisia daci biyu da daya a wasansu na birnin Alkahira.

Mohamed Fadl da Ahmed Fathi ne suka ciwa Al Ahly kwallayenta a yayinda kaptin din Esperance Oussama Darragi ya farke guda.

Nan da makwanni biyu ne za ayi bugu na biyu na wasannin zagayen kusada karshen.