Capello ya gayyaci Kevin Davies cikin tawagar Ingila

Davies
Image caption Kevin Davies a baya ya cire ran bugawa Ingila

Kocin Ingila Fabio Capello ya kira dan kwallon Bolton wanda ba a taba kira ba wato Kevin Davies cikin tawagar 'yan kwallon da zasu buga wasan share fage na neman cancantar buga gasar cin kofin kasashen Turai.

Ingila zata kara da Montenegro a filin wasa na Wembley a ranar 12 ga watan Oktoba:

Davies me shekaru 33 zai hade da Wayne Rooney da Darren Bent da Peter Crouch a gaban Ingila.

Tawagar 'yan kwallon Ingila:

Gola: Ben Foster (Birmingham City), Robert Green (West Ham United), Joe Hart (Manchester City)

'Yan kwallon baya:

Ashley Cole (Chelsea), Phil Jagielka (Everton), Glen Johnson (Liverpool), Rio Ferdinand (Manchester United), Joleon Lescott (Manchester City), John Terry (Chelsea), Stephen Warnock (Aston Villa)

'Yan kwallon tsakiya:

Gareth Barry (Manchester City), Joe Cole (Liverpool), Steven Gerrard (Liverpool), Tom Huddlestone (Tottenham Hotspur), Adam Johnson (Manchester City), Aaron Lennon (Tottenham Hotspur), Jack Wilshere (Arsenal), Shaun Wright-Phillips (Manchester City), Ashley Young (Aston Villa)

'Yan kwallo gaba:

Darren Bent (Sunderland), Peter Crouch (Tottenham Hotspur), Kevin Davies (Bolton Wanderers), Wayne Rooney (Manchester United)