Hodgson:Muna kokari kada mu nutse a gasar premier

Hodgson
Image caption Hodgson na cikin damuwa akan makomar Liverpool

Kocin Liverpool Roy Hodgson ya amince kungiyarshi a halin yanzu na kokarin kada ta nutse a gasar premier amma dai abinda yafi damunshi shine rashin haskakawar 'yan kwallonshi.

Blackpool ta doke Liverpool a Anfield daci biyu da daya kuma a itace ta uku daga can kasan teburin premier.

Hodgson yace: "akwai sauran wasanni talatin da daya amma dai muna kokarin kada mu nutse ne".

Ya kara da cewar"a gaskiya abinda yafi damuna shine 'yan wasana basa taka leda yadda ya kamata".

A halin yanzu dai cikin wasanni bakwai, Liverpool tana da maki shida ne kacal.