Dan Chelsea Alex zai shafe makwanni uku yana jinya

Alex
Image caption Alex da Drogba suna murnar nasarar da suka samu

Dan kwallon bayan Chelsea Alex zai shafe makwanni uku baya taka leda saboda ya raunata cinyarshi a wasan dasu ka doke Arsenal daci biyu da nema.

Dan shekaru ashirin da takwas ya zira kwallo a cikin minti na tamanin da biyar kuma dashi aka kamalla wasan.

Dan kwallon Brazil din kuma ya janye daga wasan sada zumuncin da kasarshi za ta buga da Iran a ranar Alhamis da kuma Ukraine a ranar Litinin.

Watakila kuma ba zai buga Chelsea da Aston Villa da Spartak Moscow.

An siyo Alex ne daga PSV Eindhoven a 2007,kuma ya kasance dan wasan da Kocin Chelsea Carlo Ancelotti tare da John Terry a tsakiyar Chelsea.

A kakar wasa ta bana, Alex ya buga duka wasannin Chelsea a yayinda kungiyar ke kokarin kare kofinta.