Zan iya sake komawa taka leda a gasar premiership-Forlan

Forlan
Image caption Diego Forlan a lokacin da ya samu kyauta a Turai

Dan kwallon Atletico Madrid na kasar Uruguaya Diego Forlan ya ce ya shirya komawa taka leda a gasar premiership ta Ingila idan har aka yi mashi tayin daya dace.

Forlan wanda aka zaba gwarzon dan kwallon gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu ya shafa leda a Manchester United kafin a siyar dashi zuwa Athletico a shekara ta 2007 akan Euro miliyan 21.

Ya shaidawa wata jarida a Spain cewar "naji dadin zaman dana yi a Ingila, kuma idan na kara samun dama zan iya komawa".

Forlan ya kasance kashin bayan Atletico Madrid inda suka lashe gasar Europa League a kakar data wuce inda suka doke Fulham a wasan karshe daci biyu da daya.

Dan shekaru 31, Forlan sau biyu yana samun kyautar dan kwallon da yafi kowanne cin kwallaye a gasar La Liga sannan kuma sau biyu ana bashi kyautar takalmin kwallon zinare na Turai.