Newcastle ta kai karar De Jong wajen hukumar FA

De Jong
Image caption Nigel De Jong ya karya kafar Hatem Ben Arfa.

Kungiyar Newcastle ta rubutawa hukumar dake kula da gasar premier ta Ingila wato FA akan cewar ta dauki hukuncin daya dace akan Nigel de Jong saboda karya kafar dan kwallonta Hatem Ben Arfa.

Dan kwallon Newcastle din an yimashi gyaran karaya sakamakon taho mu gama da De Jong da suka yi a ranar Lahadi inda suka sha kashi wajen Manchester City daci biyu da daya.

Newcastle ta ce ya kamata FA ta kara duba gamuwan, saboda alkalin wasa Martin Atkinson bai hukunta dan kwalllon.

A cewar kungiyar"De Jong yayi amfani da karfin daya wuce kima".

A halin yanzu dai an cire De Jong n tawagar Netherlands da zata kara da Moldova da Sweden,sannan kuma kocin kasarshi Bert van Marwijk yace zai gana da dan kwallon akan yadda yake kai hari a kwallo.