Fernando Torres ya kara turgudewa

Torres
Image caption Fernando Torres ya shiga rudu

Akwai shakku dan kwallon Liverpool Fernando Torres ba zai taka leda ba a wasansu da Everton na ranar 17 ga watan Oktoba saboda rauni.

Dan shekaru 26 ya buga wasa na minti goma ne kacal a wasan da Blackpool ta doke Liverpool daci biyu da daya.

Har wa yau an cire Torres cikin tawagar Spain wacce zata kara da Lithuania da kuma Scotland a wasan share fage na neman cancantar buga gasar kwallon kasashen Turai.

Likitan Liverpool Dr Peter Brukner ya ce" Fernando zai bukaci magani daga nan zuwa makwanni masu zuwa".

Raunin da Torres ya samu a yanzu shine irin wanda ya ji a gasar cin kofin duniya a wasan Spain da Holland a watan Yuli abinda kuma ya janyo ba a fara taka leda ba a farkon gasar premier.