Watakila Steve McClaren ya kara zama kocin Ingila

McClaren
Image caption Steve McClaren na tunanin maye gurbin Fabio Capello

Darektan bunkasa kwallon kafa a hukumar kwallon Ingila-FA Trevor Brooking ya ce watakila Steve McClaren ya sake kara zama kocin tawagar 'yan kwallon Ingila.

McClaren ya jagoranci Ingila na watanni 17 kafin a koreshi saboda ya kasa tsallakewa da Ingila zuwa gasar kwallon Turai a 2008.

Amma bayan nan ya jagoranci kungiyar FC Twente ta lashe gasar kasar Holland kuma a yanzu shine kocin kungiyar Wolfsburg ta Jamus.

Brooking yace"idan har ya cigaba da samun nasara, zamu saka sunanshi cikin wadanda za a iya baiwa mukamin".

Kocin Ingila na yanzu Fabio Capello ya ce zai bar mukamin bayan gasar kwallon Turai a 2012.

A baya dai kocin Spurs Harry Redknapp dana Blackburn Sam Allardyce dana Sunderland Steve Bruce, da Roy Hodgson na Liverpool da Martin O'Neill duk anata alakantasu da maye gurbin Capello.