Najeriya ta maido da korar jami'in NFF

Kaita
Image caption Sani Kaita a lokacin da aka bashi jan kati a Afrika ta Kudu

Najeriya ta maido da korarren sakatare janar na hukumar Nff Musa Amadu a wani matakin jawo hankalin Fifa ta canza hukuncinta.

A ranar Litinin ne Fifa ta dakatar da Najeriya daga shiga kwallon kafa saboda zargin gwamnati na tsoma baki a cikin harkar.

A watan daya gabata ne dai hukumar wasanni na Najeriya ta kori Amadu daga kan kujerarsa abinda kuma bai yiwa Fifa dadi ba.

A ranar Talata ne ya koma kan mukaminshi don cika daya daga cikin ka'idojin da Fifa ta gindaya.

Kakakin Nff Robinson Okosun ya shaidawa BBC cewar"tabbas sakatare janar Musa Amadu ya dawo ofis kuma har ya fara aiki gadan gadan".

Komowa aikin Amadu ya sa an fara tunanin watakila Fifa ta sauya hukuncinta akan Najeriya don ta samu damar buga wasanta da Guinea a ranar Lahadi don wasan cancantar buga gasar cin kofin Afrika a 2012.