Marsielle na neman shigar da kara akan Nigel De Jong

De Jong
Bayanan hoto,

Dan kwallon Manchester City Nigel de Jong

Kungiyar Marseille ta Faransa ta ce zata shigar da kara akan dan kwallon Manchester City Nigel de Jong bayan ya karya kafar dan kwallon Newcastle Hatem Ben Arfa a taho mu gamar da suka yi.

Ben Arfa ya bar Marseille don kasancewa dan kwallon wucin gadi a City kuma zai shafe lokaci mai tsawo yana jinya sakamakon karaya biyu daya ji.

Shugaban Marseile Jean-Claude Dassier ya bayyana cewar: "zamu shigar da kara akan De Jong".

Duk da cewar ba a hukunta De Jong ba a wasan da Manchester City ta doke Newcastle daci biyu da daya a ranar uku ga watan Oktoba, amma dai an cire shi daga tawagar Netherlands wacce ta kara da Moldova a ranar Juma'ar data wuce da kuma wasansu da Sweden a ranar Talata bayanda kocinsa Bert van Marwijk yace "irin wannan nuna karfin baida amfani".

Newcastle dai tuni ta aikewa hukumar kwallon Ingila FA akan cewar ya kamata a dauki hukunci akan De Jong don kaucewa aukuwar irin haka a nan gaba.