FIFA ta baiwa Togo makwanni ta gudanar da zabe

Obilale
Image caption Golan Togo Kodjovi Obilale

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA at baiwa hukumar kwallon Togo karin makwani uku don gudanar da zaben sabbin shugabanninta.

FIFA ta ce ta amince da bukatar Togo na neman karin lokaci kafin a gudanar da zaben saboda shugaban kwallon Togo Seyi Memene ya tafi kasar waje neman magani.

FIFA ta ce dole ne a gudanar da zaben a ranar shida ga watan Nuwamba ko kuma a dakatar da Togo daga shiga gasar kwallon kafa a duniya.

A watan Disamba bara ne FIFA ta kafa kwamitin riko na hukumar kwallon Togon bayan da aka samu rashin jituwa a tsakanin shugabannin hukumar.

Bugu da kari a watan daya gabata ne akayi wani abun kunya inda aka kai tawagar bugi daga Togo suka kara da Bahrain.