Liverpool ta samu sabon tayi akan pan miliyan 320

Liverpool
Image caption Tambarin Liverpool

Wani attajiri dan kasar Singapore Peter Lim ya yi tayin sayen kungiyar Liverpool da kaddarorinta akan pan miliyan dari uku da ashirin.

Wannan tayin ya wuce pan miliyan dari uku da kamfanin New England Sports Ventures (NESV) wanda shugaban Liverpool Martin Broughton ya amince a makon daya gabata.

Editan dake kula da kasuwanci Robert Peston ya ce Mista Lim ya kuma yi alkawarin bada pan miliyan arba'in don siyo sabbin 'yan kwallo.

Peston ya kara da cewar da yuwa 'yan kwamitin gudanarwa na Liverpool sun iya kaucewa sabon tayin.

Mista Lim a wata sanarwa ya ce:"Ina mutunta da kuma sha'awar kungiyar Liverpool wanda keda tarihi sosai.Kuma na sha alwashin sake kawo cigaba a kungiyar".