An kwacewa 'yar Najeriya Osayemi kyautar zinare

Osayemi
Image caption Osayemi murna ta koma ciki

An kwacewa 'yar Najeriya Damola Osayemi kyautar zinaren data lashe a tseren mita dari a gasar common wealth saboda ta sha haramtaccen kyawa mai kara kuzari.

Akan haka dai an baiwa 'yar Ingila Katherine Endacott kyautar zinaren.

Tun da farko dai 'yar Australia Sally Pearson ce ta kamalla a matsayin ta farko amma aka hana ta kyautar saboda tafka kuskuren data yi.

Natasha Mayers ta kasar St Vincent and the Grenadines an bata kyautar azurfan sai kuma Delphine Atangana ta Kamaru wacce aka baiwa tagulla.