Owen Hargreaves zai komo fagen fama a United

Hargreaves da Ferguson
Image caption Owen Hargreaves tare da Sir Alex Feguson

Owen Hargreaves zai komo bugawa Manchester United kwallo bayan shafe lokaci mai tsawo yana jinyar rauni a gwiwarshi.

Ana saran Hargreaves zai taka leda a wasan United da West Brom na ranar Asabar.

Dan shekaru 29, dan kwallon tun a watan Satumban 2008 rabon shi da a fara wasa dashi saboda matsannancin ciwon gwiwa.

Likitan 'yan kwallon United Dokta Richard Steadman ya ce "Owen zai iya buga wasa kadan a ranar Asabar".

An yiwa dan kwallon Ingilan tiyata a gwiwarshi a kasar Amurka a shekara ta 2008 amma yana fuskantar matsala wajen warkewa.

Hargreaves ya koma United daga Bayern Munich a watan Yulin 2007 kuma tun a watan Mayu rabon daya taka leda a kungiyar.