Dan Najeriya Obasi zai koma taka leda a karshen mako

Obasi
Image caption Chinedu Obasi ya yi jinya ta makwanni hudu

Dan kwallon Najeriya Chinedu Obasi zai koma taka leda a kungiyarshi Hoffenheim a karshen wannan makon bayan ya shafe makwanni hudu yana jinya.

Obasi ya karya kafa ne amma watakila ya buga wasansu da Borussia Mönchengladbach a ranar Lahadi.

Obasi ya shaidawa BBC cewar "na kusa warwarewa na kosa in taka leda a karshen wannan makon".

Dan kwallon dai ya buga duka wasannin Najeriya uku a gasar cin kofin kwallon duniya a Afrika ta Kudu amma ya nuna rashin jin dadi akan yadda hukumar NFF bata kula da raunin da yaji ba.

Obasi ya bukaci hukumar NFF ta sasanta 'ya'yanta don kaucewa matsaloli da Super Eagles ke fuskanta a halin yanzu.