2018:Sepp Blatter ya tattauna da David Cameron

Cameron da Blatter
Image caption Pirayi Ministan Birtaniya David Cameron da Shugaban Fifa Sepp Blatter

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa Sepp Blatter ya tattauna da Pirayi Ministan Birtaniya David Cameron akan batun yinkurin Ingila na daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018.

Blatter ya kalli yadda aka gabatar da kokarin Ingila da shirye shiryenta kuma ya gana da manyan jami'an kwallo da kocin Ingila Fabio Capello da wasu 'yan kwallo a ziyarar tashi a titin Downing.

Blatter ya ce "na gamsu da irin shirye shiryenku, Ingila za ta iya daukar bakuncin gasar".

A ranar biyu ga watan Disamba ne Fifa za ta sanarda inda za ayi gasar kwallon duniya na 2018 da 2022.

Ingila na takara ne a 2018 tare da Rasha da Amurka sai kuma hadin gwiwar Portgula da Spain da kuma na Belgium da Holland.