Kotu ta kara amincewa da batun sayarda Liverpool

hicks da gillette
Image caption Hicks da Gillette sun sha kasa a kotu

Hukunce-hukuncen kotu daban daban na ci gaba da haifar da rudani a yunkurin da ake yi na sayar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a Ingila.

Hukunci na baya-bayan nan shi ne wanda wata babbar kotu a London ta yanke hukuncin da ya kawar da wanda wata kotu ta yanke a Amurka, inda ta hana sayar da kungiyar.

Wannan na nufin kamfanin New England Sports Ventures, masu kungiyar Base Ball ta Boston Red Sox a Amurka, na da damar sayen kungiyar akan fan miliyan 300.

Bugu da kari wannan hukuncin ya kara janyo cikas ga masu kungiyar wato Tom Hicks da George Gillette wadanda suka kai karar don su hana cinikin.

Haka zalika wani attajirin dan kasuwa a Singapore Peter Lim ya nuna muradinshi na sayen kungiyar inda yayi tayi akan pan miliyan dari uku da ashirin.