An kammala gasar Commonwealth a India

Gasar Commonwealth a India
Image caption Daya daga cikin 'yan wasan da suka samu nasara a gasar Commonwealth ta bana

An kammala gasar kasashen Commonwealth ta bana da aka gudanar a birnin New Delhi na India tare da kade-kade da raye-raye da kuma wasannin wuta, duk da irin shakkun da aka nuna da farko.

A karshen gasar an mikawa birnin Glasgow na Scotland tutar tabbatar da cewa anan ne za a gudanar da gasar ta gaba a shekara ta 2014.

India mai masaukin baki ta taka rawar gani a ranar karshe bayanda ta maye gurbin Ingila a matsayi na biyu a gasar, yayinda Australia ta zamo ta farko.

Wakilin BBC da ke filin wasa na Jawaharlal Nehru a birnin New Delhi, ya ce an kammala wasan kamar yadda aka bude shi, inda aka rude da shewa lokacin da tawagar India ta fito.

Najeriya wacce da farko take mataki na shida ta kare a matsayi na tara.

Kawo yanzu an samu 'yan wasa hudu da laifin amfani da haramtattun kwayoyi, uku daga Najeriya daya kuma daga India.