Fernando Torres ya komo horo

Fernando Torres
Image caption Fernando Torres ya sha fama da rauni a kakar wasanni ta bana

Dan wasan Liverpool Fernando Torres, ya koma horo bayan ya yi fama da rauni, inda ake saran zai taka leda a wasan da za su kara da Everton.

Dan wasan ya samu rauni ne a wasan da Blackpool ta doke Liverpool ranar 3 ga watan Oktoba, kuma bai buga wasan da Spain ta yi da Lithuania da Scotland ba.

Sai dai bayan wata kula da aka bashi ta gaggawa, Torres, dan shekaru 26, ya fara horo ranar Laraba, kuma ana saran zai buga wasan su da Everton.

A bangare guda kuma, dan wasan Holland Dirk Kuyt, ya samu rauni a idan sahunshi a wasan da Holland ta lallasa Sweden da ci 4-1.