Sepp Blatter ya ce FIFA za ta binciki Amos Adamu

Adamu
Image caption Ana zargin Amos Adamu da yinkurin sayar da kuri'a

Shugaban hukumar kula da wasan kwallon kafa ta duniya, FIFA, Sepp Blatter ya dauki alkawarin gudanar da bincike akan zargin cin hanci da rashawa akan wasu manyan jami'an hukumar biyu.

Jaridar Sunday Times, ce ta wallafa cewar Mr Amos Adamu, wakili a kwamitin gudanarwa na hukumar, wanda ya fito daga Nigeria da kuma Reynold Temarii dan Kasar Tahiti, dukkaninsu sun nuna a shirye su ke su sayar da kuri'ar su ta zabar kasar da zata karbi bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a shekarar ta 2018 da kuma na 2022.

Jaridar ta ce, Mr Adamu ya bukaci a bashi dala dubu dari takwas don ya gina filayen wasa a Najeriya, da aka tambaye shi yana gani idan a ka bashi kudi don gudanar da aikin kashin kansa hakan za ta sa ya sauya yadda zai kada kuri'a, sai ya ce, ''lallai hakan zai yi tasiri.Tabbas kuwa''.

Ya shaidawa 'yan jaridar cewa shi za a baiwa kudin, ba gwamnatin kasarsa ba.

Ya kara da cewa, yana neman hanyar da zai samu kudi kimanin fan dari biyar don gina filayen wasa.

Jaridar ta kuma yi zargin cewa shi ma Reynald Temarii, wanda shi ne shugaban wata gamammiyar kungiyar kwallon kafa, ya tattauna batun biyan sa kudi don gina wata makarantar koyar da wasanni.

Sai dai FIFA ta ce, ta sa ido sosai kan yadda a ke kokawar ganin an dauki nauyin gudanar da gasar, kuma za ta tankade-da rairaye duk wani al'amari kan batun.