Wayne Rooney zai bar Manchester United-Ferguson

Rooney
Image caption Wayne Rooney na takun saka tsakaninshi da Sir Alex Ferguson

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya tabbatar da cewa Wayne Rooney na son barin kungiyar kuma ba zai sabunta kwangilarshi ba.

Ferguson din ya tabbatar cewa ya 'girgiza' kuma abun kunya ne ace Rooney na son tafiya, amma dai bashi da matsala da dan kwallon Ingilan mai shekaru ashirin da hudu da haihuwa.

Ya kara da cewar"har yanzu kofarmu a bude take idan yanason cigaba da taka leda a Old Traford".

A halin yanzu Rooney ya raunata idon sawunshi abinda kuma yasa ba zai taka leda ba a wasansu da Bursaspor na ranar Laraba a gasar zakarun Turai.

Yarjejeniya tsakanin Rooney da Manchester United za ta kare ne a shekara ta 2012.