Essien zai komo Black Stars a watan Maris na badi

Essien
Image caption Micheal Essien sanye da kambum kaptin din Ghana

Michael Essien ya ce zai koma takawa kasarshi Ghana kwallo a wasanta na share fagen neman buga gasar cin kofin Afrika tsakaninta da Congo a watan Maris din badi.

Dan kwallon Chelsea din ya dakata daga bugawa Black Stars kwallo tun a watan Agusta bayan ya murmure daga jinya mai tsawo.

Tun a gasar cin kofin kasashen Afrika a Angola a watan Junairun bana rabonda Essien ya takawa Ghana keda.

Raunin daya ji a gwiwarshi a wasan Ghana na farko ya janyo mashi jinya mai tsawo har ya kasa zuwa gasar cin kofin duniya a 2010 a Afrika ta Kudu.

Amma dai a halin yanzu hukumar dake kula da kwallon kafa a Ghana GFA ta ce Essien zai buga wasansu da Congo Brazzaville.

Shugaban GFA Kwesi Nyantakyi ya ce"Essien zai komo fagen fama a watan Maris na badi".