Arsenal ta samu kanta - Ivan Gazidis

Arsenal
Image caption Magoya bayan Arsenal na bukatar gani a kasa ta fuskar nasara

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Ivan Gazidis, ya ce kungiyar ta samu kanta ta fuskar tattalin arziki, don haka yanzu za ta maida hankali kan sayen 'yan wasa.

A watan da ya gabata kamfanin da ke da mallakin kungiyar, ya bada sanarwar samun ribar fam 56.

Sannan ta ce ta biya dukkan basussukan da ake binta dangane da rukunin gidajen da ta gina a tsohon filin wasa na Highbury.

Bashin kawai da ya rage shi ne na sabon filin wasan da ta gina na Emirates.

Cin gashin kai

"Wannan ba karamin aiki bane, amma a karshe mun samun 'yancin kanmu," a cewar Mista Gazidis, lokacin da yake magana a wurin taron kungiyar na shekara-shekara.

Ya kara da cewa "yanzu ba ma bukatar mu dogara da kowa a nan gaba. Sai dai akwai bukatar dorewa kan wannan nasarar."

A yanzu dai mutum hudu ne suka fi kowa yawan hannun jari a Arsenal, kuma dukkansu sun goyi bayan sabon tsarin da kungiyar ke kai.