Hodgson ya ce ba zai ajiye aikinsa ba

Kocin Liverpool Roy Hodgson ya ce ba zai ajiye aikinsa ba duk da cewa kungiyar bata taka rawar gani ba a kakar wasan bana, ya zuwa yanzu.

A yanzu haka dai kungiyar ce ta goma sha tara a gasar Premier a yayinda ta lashe wasa guda daya tilo cikin wasanni takwas da ta buga a kakar wasan bana a gasar.

Harwayau kungiyar ce ke jagorancin rukunin da take a gasar Europa bayan ta buga canjaras da Napoli a wasan da kungiyoyin biyu su ka buga a ranar alhamis.

"Ban taba tunanin ajiye aikina ba, kuma ba zan yi hakan ba. Zan jima ina aiki da kungiyar". In ji Hodgson.

"Na kama aiki ne a kungiyar domin in taimaka mata, kuma ina ganin 'yan wasan kungiyar na goyon bayana dari bisa dari a kokari na wajen habaka kungiyar".