Rooney ya sa hannu a sabon kwantaragi a Manchester United

Dan wasan Manchester United Wayne Rooney, ya yi amai ya lashe, a yayinda ya sanya hannu a sabon kwantaragi na tsawon shekaru biyar da kulob din.

A farkon makon da ke karewa ne, dan wasan mai shekaru ashirin da hudu a duniya ya bayyana aniyarsa na barin kungiyar, inda ya ce bai gamsu da yadda ake tafiyar da kungiyar kwallon kafa ba, musamman wajen siyan kwarrarrun 'yan wasa.

A yanzu Wayne Rooney zai taka wa kungiyar leda har zuwa shekarar 2015.

Bayan dan wasan ya tattauna da kungiyar, ya nuna farin cikinsa na ci gaba da takawa kungiyar leda.

"Na tattauna da hukumomi a kungiyar da kuma mai horar da 'yan wasan kungiyar kuma duk sun bani kwarin gwiwar zama a kungiyar", in ji Rooney.

Shi ma mai horas da 'yan wasan kulob din Sir Alex Ferguson, ya ce: "Ina Murna Wayne ya amince ya ci gaba da zama a Manchester United."