Arsenal ta casa Manchester City daci uku da nema

Arsenal
Image caption 'Yan Arsenal na murnar doke Manchester City

Kwallayen da Samir Nasri da Alex Song da Nicklas Bendtner suka ciwa Arsenal ne ya bata damar doke abokiyar hammayarta Manchester City a fili wasa na Eastlands.

City dai ta shiga rudu bayan da aka kori Dedryk Boyata 'yan mintuna da faran wasan.

Arsenal a yanzu ta zama ta biyu akan teburi inda Chelsea ta fita da maki biyar bayan da Chelsea din ta samu galaba akan Wolves daci biyu da nema.

Sakamakon sauran karawar:

*Stoke City 1 - 2 Manchester United *Liverpool 2 - 1 Blackburn Rovers *Tottenham Hotspur 1 - 1 Everton *Birmingham City 2 - 0 Blackpool *Chelsea 2 - 0 Wolverhampton *Sunderland 1 - 0 Aston Villa *West Bromwich 2 - 1 Fulham *Wigan Athletic 1 - 1 Bolton Wanderers *West Ham United 1 - 2 Newcastle United