Platini ya soki batun saka fasaha a kwallon kafa

Platini
Image caption Michel Platini ya hau kujerar UEFA tun a 2006

Shugaban hukumar dake kula da kwallon Turai Uefa Michel Platini ya ce saka na'urar fasaha wajen tattance shigar kwallo a raga zai maida kwallo tamkar wasan kwaikwayo.

Fifa ta bayyan cewar za ta sake duba batun tattaunawa akan lamarin,amma dai Platini ya nuna cewar saka mataimakin alkalin wasa a bayan kowane raga shine zai magance matsalar.

Platini yace"dole ne sai klub klub da magoya baya da 'yan wasa da kafafen yada labarai sun taimakawa alkalan wasa".

Ya kara da cewar "a yanzu tsarin da muke bi a gasar zakarun Turai kenan".

A makon daya gabata ne dai kwamitin dake kafa dokokin kwallo IFAB ya bukaci kamfanoni sun bada shawararinsu akan yadda batun saka fasaha a bayan raga daga nan zuwa watan Nuwamban bana.