2018: Ingila ta kai karar shugaban 'Russia 2018'

World cup
Image caption Ingila da Rasha na takara akan gasar cin kofin duniya a 2018

Tawagar dake kokarin nemawa Ingila damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018 wato 'England 2018' ta kai karar shugaban tawagar hammayarta na Rasha saboda kalaman da yayi akan London.

Shugaban Rasha 2018 Andrei Sorokin an ambato shi yana sukar London cewar ana aikata miyagun laifuka sannan matasan birnin nada dabi'ar shan barasa fiye da kima.

Fifa dai ta haramta sukar juna daga wajen kasashen dake hammaya na kokarin daukar bakuncin gasar cin kofin duniya.

Sorokin ya ce ba a fassara kamalanshi dai dai ba, amma kuma yace tawagar Ingila na son a nemi afuwa daga wajenta ne.