Tottenham ta sayi dan Afrika ta Kudu Bongani Khumalo

Khumalo
Image caption Bongani khumalo ya takawa Afrika ta kudu kwallo a gasar kofin duniya

Kungiyar Tottenham ta Ingila ta kamalla yarjejeniyar sayen dan kwallon Afrika ta Kudu Bongani Khumalo bayan ya samu nasara a gwajin da akayi mashi a White Hart Lane.

Dan shekaru 23, Khumalo ya buga gasar cin kofin duniya kuma a baya Rangers ta nuna sha'awa akanshi, amma a yanzu zai koma Spurs ne daga Super Sports United akan pan miliyan daya da rabi a watan Junairun badi.

Amma dai za a sanya hannu a kwangilar ce idan ya samu takardar izinin taka leda a Ingila.

KocinTottenham Harry Redknapp ya ce "muna son shi mun gwada shi kuma baida tsada".

An haifi Khumalo ne a Swaziland sannan ya buga duka wassanin Afrika ta Kudu guda uku a gasar cin kofin duniya inda ya zira kwallo a wasan da kasarshi ta doke Faransa daci biyu da daya. Zuwan dan kwallon zai karawa bayan Tottenham karfi gannin cewar Michael Dawson da Jonathan Woodgate zasu shafe lokaci mai tsawo suna jinya.