Blanc ya yi kira a rage yawan klub a gasar Faransa

Blanc
Image caption Kocin Faransa Laurent Blanc nada babban kalubale gabanshi

Kocin 'yan kwallon Faransa Laurent Blanc ya shiga sawun kiraye kirayen da ake yiwa mahukunta kwallon kafa a kasar na cewar su rage yawan klub klub na babbar gasar kasar daga 20 zuwa 18.

Blanc, wanda ya samu goyon bayan shugabannin klub klub na kasar, ya bayyana cewar rage yawan kungiyoyi a gasar zai taimaka a karfafa tawagar dake wakiltar Faransa a kwallo.

Blanc ya shaidawa jaridar L'Equipe cewar " idan har munason maido da karfin tawagarmu, tabbas sai mun gyara tsarin jadawalin kwallon gasarmu".

A ganinshi dai hakan zai sa a kaucewa matsalar da Faransa ta fuskanta a gasar cin kofin duniya inda bata samu nasara a duka wasanninta uku ba.

Tun bayan yakin duniya na biyu ne dai ake ta cancanja yawan kungiyoyi a babbar gasar Faransa daga 18 zuwa 20, amma na baya bayannan ne shine a 2002 inda aka kara yawansu daga 18 zuwa 20.