An kori shugabar Hukumar kwallon Zimbabwe

Shugabar hukumar kwallon Zimbabwe
Image caption Henrietta Rushwaya ta dade tana fuskantar kalubale

Hukumomi a Zimbabwe sun kori shugabar hukumar kwallon kasar (zifa), Henrietta Rushwaya, daga kan mukaminta.

A ranar Talata ne jami'an Zifa suka kori Rushwaya, bayanda ta tura kungiyar kwallon kasar ta buga wasu wasanni a nahiyar Asia.

Wani kwamitin bincike ya same ta da laifin almubazzaranci da kuma rashin da'a da sauransu.

Sai dai an dage zargin da aka yi mata na sayarda wasa a ziyarar da tawagar kasar takai yankin Asia a watan Disamba, har sai an gudanar da karin bincike.

An kuma same ta da laifin karbar bashin kudade daga hukumar wasanni ta Sports and Recreation Commission, wadanda suka yi layar zana. A watan Yulin da ya gabata ne aka dakatar da Rushwaya, bayanda ta shirya ziyarar da 'yan kwallon kasar suka kai kasashen Thailand da Syria da Malaysia a watan Disamban bara.