Paul Ince ne sabon kocin Notts County

Paul Ince
Image caption Sabon kocin Notts County Paul Ince

Kungiyar Notts County da ke matakin League One a Ingila, ta tabbatar da nadin tsohon dan wasan Ingila Paul Ince a matsayin sabon kocinta.

Ince, wanda ya yi murabus daga kungiyar MK Dons a watan Mayu, ya maye gurbin Craig Short, wanda aka kora ranar Lahadi, kasa da watanni shida da nada shi. Tsohon kociyan Macclesfield da Blackburn Ince, mai shekaru 43, ya zamo koci na shida da kungiyar ta Notts County ta nada a cikin shekara guda.

Ian McParland da Hans Backe da Dave Kevan da Steve Cotterill duka sun yi aiki a kulob din daga watan Oktoban bara.

Shugaban kulob din Ray Trew ya gayawa shafin intanet na kungiyar cewa: "Paul ya nuna kwarewa sosai a lokacin da yake taka leda da kuma shekarun da yayi yana aikin koci, abinda yasa na zabe shi."