Rooney zai dade bai dawo fagen daga ba-Ferguson

Rooney da Ferguson
Image caption A makwon da ya gabata ne Rooney ya kulla sabuwar yarjejeniya da United

Kociyan Manchester United Sir Alex Ferguson, ya ce Wayne Rooney zai dade bai dawo taka leda ba, sakamakon raunin da ya ke fama da shi.

Dan wasan mai shekaru 25, yanzu haka yana hutu inda yake murmurewa daga raunin da ya samu a idon sahunshi.

Rooney wanda kwanan nan yasa hannu kan sabuwar yarjejeniyar shekaru biyar bayan ya bayyana cewa yana son barin kungiyar.

Da aka tambayi Ferguson ko makwanni uku sun ishi dan wasan ya murmure, sai yace: "Ina ganin zai shafe fiye da haka."

Rooney, wanda yake ci gaba da murmurewa a hotun da yake yi a kasar Dubai tare da matarsa Coleen, bai buga wasanni ukun baya da United ta yi ba.

Rabon da dan wasan ya takawa United leda tun ranar 16 ga watan Oktoba a karawar da suka yi da West Brom, inda aka ta shi 2-2.