Za a yi wasanni biyu ba Tavez

Carlos Tavez
Image caption Carlos Tavez yana taka rawa sosai a Manchester City

Kyaftin din Manchester City Carlos Tavez ba zai buga wasan da kungiyar za ta kara da Wolves a Premier da kuma Lech Poznan a gasar Europa ba, saboda rauni.

An cire dan wasan na Argentina a wasan da City ta sha kashi da ci 3-0 a hannun Arsenal ranar Lahadi, sakamakon raunin da ya samu a kafa.

Kociyan City Roberto Mancini ya baiwa dan wasan damar tafiya gida a lokacin da yake ci gaba da murmurewa, yana mai cewa: "A yanzu yana Argentina saboda matsalar cikin gida."

A farkon makwan nan, dan gaban City Roque Santa Cruz yace Tavez ba ya jin dadi kuma ya so ya bar kungiyar, amma Mancini ya yi watsi da kalaman nasa.