Golf: Lee Westwood ne na daya a duniya

Lee Westwood
Image caption Lee Westwood ne Bature na farko da ya samu matsayin tun 1994

Dan Ingila Lee Westwood ya zamo na daya a duniya a gasar Golf a karon farko, abinda ya kawo karshen makwanni 281 da dan Amurka Tiger Woods ya shafe a kan matsayin.

Dan Jamus Martin Kaymer ne ya barar da damarsa ta dare kan wannan matsayi, bayanda ya kare a mataki na hudu a gasar Valderrama da aka kammala ranar Lahadi.

Westwood, mai shekaru 37, ya zamo Bature na farko da ya hau matsayi na daya tun bayan Nick Faldo da ya samu matsayin a shekara ta 1994.

Ba Amerike Tiger Woods, ya dade yana fuskantar koma baya, tun bayan da ya samu kansa cikin rudani kan alakarsa da iyalinsa.