Lazio ta kara tazara a Serie A ta Italiya

Lazio
Image caption A kwanakin baya ba a jin duriyar Lazio, amma yanzu ta yunkuro

Lazio na ci gaba da haskakawa a gasar Serie A ta Italiya, bayan da ta makure Palermo har gida da ci daya mai ban haushi.

Hakan ya bata damar kara tazarar da ta bayar a saman tebur inda yanzu take da maki 22.

Inter Milan wacce ta doke Genoa da ci daya da nema, itace ke biye mata da maki 18.

AC Milan wacce ada take mataki na biyu, yanzu ta dawo na uku bayanda ta sha kashi a gidanta a hannun Juventus da ci 2-1. Juventus ce ta hudu a kan tebur.

Sakamakon karshen mako na Serie A

Genoa - Inter Milan 0 - 1 Roma - Lecce 2 - 0 Milan - Juventus 1 - 2 Palermo - Lazio 0 - 1 Bari - Udinese 0 - 1 Cesena - Sampdoria 0 - 0 Cagliari - Bologna 0 - 0 Brescia - Napoli 0 - 0 Parma - Chievo 0 - 0