Man City ta sha kashi a hannun Wolves

Kociyan Mancini
Image caption Kociyan Man City Roberto Mancini yana tsaka mai wuya

Manchester City ta sha kashi a hannun Wolves da ci 2-1 a gasar Premier ta Ingila a karshen mako. Har yanzu dai City ce ta hudu a kan tebur da maki 17.

Chelsea ta ci gaba da rike matsayinta na daya a gasar ta Premier da maki 25, bayan da ta lashe Blackburn Rovers da ci 2-1.

Arsenal da Manchester United ne ke biye mata da maki 20-20. Bayan da Arsenal din ta doke West Ham da ci daya mai ban haushi.

Ita ma Manchester United din ta lashe Tottenham da ci 2-0 a filin wasanta na Old Trafford.

Wasu daga cikin sakamakon karshen mako

Aston Villa 0-0 Birmingham Arsenal 1-0 West Ham Blackburn 1-2 Chelsea Everton 1-0 Stoke Fulham 2-0 Wigan Man Utd 2-0 Tottenham Wolverhampton 2-1 Man City