Rooney zai shafe makwanni 5 baya taka leda

Rooney
Image caption Rooney ya taka rawa sosai a kakar wasan da ta gabata

Dan wasan Manchester United Wayne Rooney zai shafe makwanni biyar baya taka leda, kamar yadda kociyansa Sir Alex Ferguson ya bayyana.

Dan wasan mai shekaru 25, wanda ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragin shekaru biyar, yana murmurewa ne daga raunin da ya samu a idon sahunshi wanda ya ji ranar 19 ga watan Oktoba.

"Ina ganin Rooney zai shafe makwanni biyar baya taka leda," kamar yadda Alex Ferguson ya shaida wa Sunday Express.

"Akwai bukatar ya murmure sosai. Kuma ina ganin sati biyar ya yi masa."

Da farko an zaci dan wasan zai shafe makwanni uku ne, inda aka saran zai taka leda a karawar United da Manchester City ranar 10 ga watan Nuwamba.