AWC: Najeriya ta lallasa Mali da 5-0

Image caption Tawagar Falcons

Tawagar Falcons ta Najeriya ta lallasa Mali da ci biyar da nema a gasar cin kofin Afrika ta mata da kasar Afrika ta karban bakonci.

Kungiyoyi biyu dai sun buga wasan ne a rukunin A.

A ranar lahadi, kasar Afrika ta kudu ta yi galaba a kan Tanzania da ci biyu da guda a rukunin na A.

Najeriya za ta kara ne da Afrika ta kudu ranar alhamis.

Tawagar Falcons ta Najeriya ta lashe gasar, har sau hudu a baya.