Toure ya nemi Man City ta kara nuna kwazo

Image caption Kolo Toure

Dan wasan bayan Manchester City Kolo Toure ya yi kira ga takwarorinsa a kungiyar da su kara nuna kwazo bayan kungiyar ta sha kashi a wasanni biyu a jere.

A ranar asabar din data wuce ne Wolves ta doke Manchester City da ci biyu da guda, sai kuma wasan da kungiyar ta buga da Arsenal a ranar 6 ga watan Okutoba, inda Arsenal ta lallasa ta da ci uku da nema.

A yanzu haka dai, kocin kungiyar Roberto Mancini na fuskantar matsin lamba game da rashin nasarorin da kungiyar ta samu.

"Kamata ya yi 'yan wasa su dauki nauyi fidda kungiyar kunya" In ji Toure.

"Idan kana takawa kungiyar da ta fi kowacce kudi a duniya, dolene ka nuna kwarewarka a filin wasa."

City ta lashe wasanni biyar cikin goma ne da ta buga a kakar wasan bana a gasar Premier, kuma Chelsea mai jagoranci a kan tebur ta tsere mata ne da maki takwas. Kungiyar City dai ta kashe mukudan kudade a kakar wasan bana, wajen siyan kwarrarun 'yan wasa.