Redknapp ya yi barazanar kauracewa manema labarai

Kocin Tottenham Harry Redknap ya yi barazanar kauracewa hira da manema labarai muddin hukumar FA ta Ingila ta hukunta shi.

Harry Redknap ya soki alkalin wasan daya hura wasan da kungiyar ta buga da Manchester United a ranar asabar din data gabata, bayan ya amincewa da kwallo na biyu da Manchester United ta zura.

Ya ce; "Ba zai yiwu ayi min tabaya a talbijin ba, kuma inki fadin gaskiya. Idan an yimin tabaya dolene in fadi gaskiya, kuma idan ba'a so muna fadin gaskiya a daina hira damu. Gakiyan al'amarin shine alkalin wasan yayi shirme".

A gobe ne dai hukumar ta FA za ta dauki mataki game da kalamun da Harry Redknapp ya yi na cewa alkalin wasan ya hura shirme a wasan saboda amincewa da yayi da kwallon da Manchester United ta zura.