Benitez ya mayardawa Hodgson Martani

Image caption Rafeal Benitez

Kocin Inter Milan Rafael Benitez ya ce Roy Hodgson ya fuskanci aikinshi no horon Liverpool ya daina sukar yadda ya tafiyar da kungiyar a lokacin da yake horon kungiyar.

A makon daya gabata ne dai, Hodgson ya soki yadda Benitez ya kashe makudan kudade wajen siyan 'yan wasa, kuma suka gagara tabuka komai.

Benitez ya ce: "Hodgson yana maganganun da bai san kansu ba."

Benitez dai ya ce Hodgson bai san yadda ake amfani da 'yan wasa ba.

Rafeal Benitez dai ya ajiye aikinshi a Liverpool a karshe kakar wasan bara, inda ya koma Inter Milan a yayinda Roy Hodgson ya koma horon kungiyar Liverpool bayan ya baro Fulham.

A yanzu haka dai Liverpool na fuskantar kalubale a gasar ta Premier, inda take na goma sha biyu a kan tebur.