Fabregas ba zai taka leda ba a gasar zakarun Turai

Image caption Cesc Fabregas

Kyaftin din Arsenal Cesc Fabregas ba zai samu taka leda ba a wasan da kungiyar za ta buga a ranar Laraba da Shakhtar Donetsk, saboda yana jinyar rauni a cinyarsa.

Kocin kungiyar Arsene Wenger, ya ce raunin baiyi tsanani ba, kuma yana fatan dan wasan zai samu damar buga wasan da kungiyar za ta yi da Newcastle a ranar Lahadi.

Wenger ya ce: "raunin baiyi muni ba, yana dan ci ciwo ne, bama son muyi kasadar sanya shi a wasa, shi yasa muka barshi ya huta."

Har wa yau akwai shakkun cewar Alex Song da Andrei Arshavin da kuma Denilson ba za su samu damar buga wasan ba.