Batista ne sabon kocin Argentina

Image caption Sergio Batista tare da shugaban kwallon kafan Argentina, Julio Grondona

Hukumar kwallon kafar Argentina ta tabbatarda nadin Sergio Batista a matsayin kocin kasar na dindindin.

Wannan dai ya fito wani zaton cewar za'a dawo da tsohon kocin kasar Diego Maradona, domin ya jagoranci tawagar kasar zuwa gasar cin kofin duniya da za'a shirya a shekarar 2014.

Batista dai ya ciwa Argentina zinari a kwallon kafa a gasar Olympic din da aka shirya a shekarar 2008.

Hukumar kwallon kafan Argentina dai a bayan ta dauki Maradona aiki a shekarar 2008 da takwas inda kuma ya jagoranci kasar zuwa gasar cin kofin duniya da kasar Afrika ta kudu ta shirya.

Maradona dai ya ajiye aikinshi ne bayan da Jamus ta lallasa Argentina a gasar da ci hudu da nema, inda yaki sa hannu a wani sabon kwantaragi.

Batista dai ya yi wasa tare da Maradona a tawagar Argentina.