Takaddama kan salalar gasar cin kofin duniya a Ghana

Image caption Ghana ta buga wasan dab da kusa dana karshe a gasar cin kofin duniya

Ana takaddama game da kudin salalar da 'yan wasan Ghana suka samu a gasar cin kofin duniya da aka yi a kasar Afrika ta kudu a watan Junairun da ya gabata.

Babu dan wasan daya samu dala 63,000 da aka yiwa musu alkawarin, saboda takaddamar da ta taso tsakanin kungiyar ta Black Stars da kuma Babban Bankin Ghana.

Babban Bakin na Ghana ya nace cewar zai biya kudaden ne a bankunan da 'yan wasan suke ajiya.

Amma 'yan wasan sunki yarda da hakan inda suke bukatar Bankin da ya biya su tsabar kudaden daga bankin a hannunsu.

A wata sanarwa da bankin ya fitar, ya ce ba zai iya biyan tsabar kudi da ya haura dala dubu goma ba, saboda ya keta ka'idodinsu.