Nani da Fletcher sun samu rauni

Image caption Nani

Nasarar da Manchester United ta yi a gasar zakarun Turai a kan Bursaspor ya zo mata da tsada inda Nani da Darren Fletcher suka samu rauni.

Manchester United dai ta yi nasara ne a wasan da ci uku da nema, a yayinda Nani ya dingisa a wasan kuma ba zai samu damar buga wasan da kungiyar za ta yi da Wolves a ranar Asabar.

Fletcher ma dai ya samu raunin ne a idon sahun shi bayan ya zura kwallon farko a wasan.

"Gaskiya bai jin dadin yadda lamarin ya faru ba, amma dai haka na faruwa, kwallon kafa ta gaji haka."

Micheal Owen da Wayne Rooney suna cikin jerin sunayen 'yan wasan da ke fama da rauni a kungiyar.