Super Eagles bata kira Enyeama da Yobo a wasan sada zumunci da Iran

Image caption Osaze a lokacin dayake takawa Najeriya leda

Hukumar kwallon kafan Najeriya bata kira Vincent Enyeama da kuma Joseph Yobo ba a wasan sada zumunci da kasar za ta buga da Iran a wannan watan.

Hukumar kwallon kafar kasar, wato Nff tace bata kira 'yan wasan biyu bane domin ta ba matasa damar nuna kansa a fagen tamoular kasar.

" Muna son mu samu sabbin jini ne a takawagar ta Super Eagles". In ji wani jami'in gudanarwa na hukumar, Emamnuel Ikpeme.

Hukumar ta Nff dai ta kira 'yan wasa 20 ne wanda daga cikinsu akwai Osaze da Victor Nsofor.

Najeriya za ta buga wasan sada zumuncin ne da Iran a ranar 17 ga wannan wata.